Kano: Babban jigo ya faɗi wanda alamu suka nuna zai samu nasara tsakanin Abba da Gawuna a kotun koli


Razaq Aderibigbe, babban jigon New Nigeria People's Party (NNPP) ya bayyana yaƙinin cewa kotun koli zata tabbatar da zabin al'ummar jihar Kano.

Mista Aderibigbe ya ce alamu sun nuna cewa alkalan kotun kolin Najeriya mutane ne masu gaskiya, waɗanda zasu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da adalci da daidaito. Legit Hausa ya wallafa.

Ɗan siyasan ya ƙara da cewa ya kamata masu riƙe da madafun iko su tuna cewa rashin adalci ke haddasa tashin yamutsi da karya doka da oda wanda ke hana ci gaba.

Jigon NNPP ya shaida wa Legit Hausa cewa:

"Duk da yunƙurin da ake na lullube gaskiya, jam'iyyar NNPP ta yi imanin cewa kotun koli zata tabbatar da muradi da zabin al'ummar Kano."

"Kotun koli za ta share duk wata tantama da ruɗani da suka baibaye hukuncin kotunan baya ba tare da tsoro ko fargaba ba."

"Mun yi imanin cewa hukuncin da kotun kolin Najeriya zata yanke zai ƙara tabbatar da zaman lafiya da tsaro da bin doka da oda a faɗin jihar Kano.

Idan baku manta ba kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamna ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jama'iyyar NNPP.

Ta kuma bayyana ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APC, Nasir Yusuf Gawuna, a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris.

Haka nan kuma Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta kori Abba daga matsayin gwamnan Kano.

Kotun ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe wacce ta tsige Abba ranar 20 ga watan Satumba, 2023

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN