‘Yan Majalisa sun nemi kama malamin da ya soki wadanda sojoji suka kashe a Maulidi


Majalisar dokokin jihar Kano ta yi magana game da kalaman da aka ji sun fito daga bakin Sheikh Baffa Hotoro a makon jiya.

An ji Usman Abubakar Tasi'u Kiru a wani bidiyo yana bayani bayan Sheikh Baffa Hotoro ya soki wadanda aka kashe a Tudun Biri. Legit Hausa ya wallafa.

A lokacin da ake jimamin mutuwar mutane kimanin 100 a wajen maulidi, malamin addin ya yi wasu maganganu da suka jawo suka.

Hon. Usman Abubakar Tasi'u Kiru mai wakiltar mazabar Kiru a majalisar Kano ya gabatar da kudirin gaggawa a kan Baffa Hotoro.

Usman Abubakar Tasi'u Kiru wanda aka fi sani da Rabula ya zargi malamin da kalaman batanci, masu ban takaici da bakin ciki.

‘Dan majalisar yake cewa duk wanda ya ji kalaman Baffa Hotoro, zai fahimci akwai tunzura jama’a a ciki da zai iya jawo rikici a kasa.

Yayin da ake makokin mutane 100 da jinyar wasu a asibiti, Hon. Usman Abubakar Tasiu ya ce kowa ya jajantawa mutanen Kaduna.

‘Dan majalisar yana ganin bai yiwuwa a sa’ilin da ake kukan wadanda aka rasa, a samu wani daga Kano yana munanan kalamai.

Rabula ya ce Kano tayi fice wajen ilmin addini a Afrika, ya kuma nuna abin da Sheikh Hotoro ya fada ya saba da koyar musulunci.

Ganin mugun tasirin abin da malamin addinin ya fada, 'dan majalisar na Kiru ya bukaci gwamnatin jihar Kano ta tuhume shi da laifi.

A ra’ayin ‘dan siyasar, sam bai dace a kamanta wadanda su ka rasu wajen zikiri da salatin Annabi Muhammad SAW da wasu fasikai ba.

Muhammadu Sanusi II ya yi fatan mutanen da su ka rasu sun yi shahada, akasin ra’ayin wasu malamai da ake zargi da zafin addini.

Bayan gabatar da kudirin, an yi zama na sirrin da a karshe ya kai ga yanke shawarar maganar ta je gaban Hisbah da majalsar shura.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN