Rahotanni da ke zuwa sun kawo cewa gobara ta tashi a ofishin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a safiyar yau Talata, 12 ga watan Disamba.
Kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X ( wanda aka fi sani da Twitter a baya) ya ce zuwa yanzu ba a tabbatar da irin barnar da gobarar da ta kama ainahn ofishin gwamnan ta yi ba.
An tattaro cewa gwamnan na a daya ofishinsa da ke sakatariyar Musa Usman lokacin da lamarin ya afku da misalin karfe 12:29 na rana. Legit Hausa ya wallafa.
An rahoto cewa an gano motocin hukumar kwana-kwana suna fita daga gidan gwamnati a kokarinsu na kashe gobarar.
Rundunar yan sanda sun hana motoci, ma’aikata da manema labarai shiga gidan gwamnatin tun daga babban kofar shiga.
From ISYAKU.COM