Wani matashi dan Najeriya ya yiwa jama'a tayin aiki mai tsoka a ofishin jakadancin Amurka da ke Lagas, Najeriya, wanda ke nuni da cewar akwai gurbin aiki na wanda zai taimaka da aikace-aikace a ma'aikatar
Wanda ya yi nasarar samun aikin zai kasance yana gudanar da ayyukansa a karkashin sashen ba da shawarwari na ma'aikatar. Legit Hausa ya wallafa.
Ayyukan da zai rinka yi sun hada da tsara ganawar jama'a da sashen ma'aikatar, samar da takardar biza ga jama'a da kuma adana bayanan duk ayyukan da ya ke yi a cikin kundin ajiyar ma'aikatar.
Albashin wannan mukamin shine ₦2,699,000 duk wata, wanda ya yi daidai da kimanin $2,500. Abun da ake bukata shine takardar shaidar kammala karatun sakandare (SSCE), amma za a fi son wadanda suka mallaki kwalayen OND, HND, ko digiri.
Za a rufe neman aikin wannan mukami a ranar 1 ga watan Fabrairun 2024.
From ISYAKU.COM