Soji sun kashe kasurgumin dan ta'adda Kachalla Ali Kawaje, Machika da kwamandodinsa 38, an kama 159


Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta tabbatar da kashe wasu fitattun kwamandojin ƴan ta'adda huɗu a hare-haren da aka kai ta sama cikin mako guda. Legit Hausa ya wallafa.

Jaridar Daily Trust ta ce ƴan ta'addan da suka baƙunci lahira sun haɗa da Haro. Dan Muhammadu, Ali Alhaji Alheri wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje da Machika.

Darakta mai kula da ayyukan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 16 ga watan Disamba a Abuja, cewar rahoton The Punch.

Buba ya bayyana cewa Machika babban ƙwararren mai haɗa bam na ƴan ta'adda ne kuma ƙanin fitaccen ɗan ta’adda (Dogo Gide) yayin da Haro da Dan Muhammadu suka ƙware wajen yin garkuwa da mutane.

Ya yi nuni da cewa, a wani farmakin haɗin gwiwa tsakanin sojojin sama da na ƙasa da suka kai hari a ranar 11 ga watan Disamba, sun kashe Kachalla Kawaje, fitaccen shugaban ƴan ta’addan da ya yi garkuwa da daliban jami’ar tarayya ta Gusau, Zamfara.

Ya ƙara da cewa an kashe Kachalla ne a ƙaramar hukumar Munya ta Nijar tare da wasu dakarunsa.

A cewarsa, sojoji suna ƙara tunkarar wasu ƴan ta'addan, kuma za su fuskanci irin abin da ya auku da su Kachalla.

Ya ƙara da cewa harin da aka kai ya yi sanadin kashe kwamandojin ƴan ta’adda sama da 38 da dakarunsu, yayin da aka kama wasu ƴan ta'adda 159.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN