Dalibin Islamiyya Alfa dan shekara 22 ya kashe kansa a jihar arewa wai saboda Allah bai amsa addu'arsa ba


Wani dalibi dan shekara 22 a makarantar Sheikh Kamaldeen Arabic da ke Ilorin a jihar Kwara ya kashe kansa.

 Dalibin mai suna Alfa Musa, an same shi ne a rataye a dakinsa da ke harabar Dagbenu a unguwar Ogidi a Ilorin a ranar Alhamis 7 ga watan Disamba, 2023.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ejire Adetoun Adeyemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa an fara bincike kan lamarin.

 PPRO ya ce marigayin ya bar wa iyayensa takardar kashe kansa watau "suicide note" .

 "Mama da baba na, ku yi hakuri, na yi haka ne saboda Allah bai amsa addu'ata ba, gwamma in mutu da in aikata zunubi, don Allah, ku gafarta mini, ina son ku, ku binne ni a gida."

 An tattaro cewa daya daga cikin abokansa ya kai ziyara gidansa a ranar da lamarin ya faru amma ya tarar da kofar dakinsa a kulle.

 Bayan an yi ta kwankwasa kofa ba tare da an ba da amsa ba, sai aka bude kofar da karfi, aka ga marigayin a rataye.

 An gan bokitin fenti da babu komai a ciki wanda ake zargin ya kife ya hau ya rataya kansa a dakinsa.

 Wani makwabcin ya bayyana marigayin wanda ya fito daga jihar Osun a matsayin musulmi mai kishin addini.

 A halin da ake ciki, daya daga cikin abokan aikinsa ya saka hoton bidiyo daga sallar jana'izar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN