Buhun shinkafa zai koma N80,000, za a yankewa wasu sanatoci daurin rai-da-rai a 2024, Malamin addini


Kamar yadda ya saba bisa al'ada, shugaban cocin INRI Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele (JP), ya saki sakonninsa game da shekarar 2024.

A hasashensa, malamin addinin ya bayyana cewa farashin shinkafa yar waje zai yi tashin gwauron zabi uwa N80,000 kan kowani buhu daya a kasar. Legit Hausa ya wallafa.

Haka kuma, babban faston ya yi hasashen cewa wasu sanatocin Najeriya za su fuskanci hukuncin daurin rai da rai a shekara mai zuwa.

Jaridar PM News ta rahoto cewa malamin addinin ya gudanar da taronsa na manema labarai na shekara a ranar Juma'a a hedkwatar cocin INRI da ke rukunin gidaje na Prosperity, Oke-Afa, Ejigbo, Lagos inda a nan ne ya yi hasashensa game da 2024.

Hasashen na kunshe ne a takarda mai shafuka 91 wanda ya saki a ranar Juma'a, 22 ga watan Disamba, 2023.

Haka kuma, ya yi hasashen cewa farashin Dala zai tashi zuwa N1400 kuma zai girgiza tattalin arziki ba da wasa ba, rahoton Daily Post.

Ya ce:

“Tattalin Arzikin Kasar zai rika canzawa ta yadda Babban Bankin Najeriya zai koka. Tallafin Gwamnati na daga cikin abubuwan da ke lalata tattalin arziki kuma babu tasirin da ya yi wajen farfado da tattalin arziki. Shinkafar gida za ta kai #45,000; Shinkafa yar waje za ta kai N80,000; lemun Coca-cola zai zama N300, kuma za a siyar da ruwan leda akan kudi biyu N100.

“Biskiti zai kai N100, N150, N200 yayin da kwalban mai zai kaii #2,000. Idan har gwamnati ba ta saurari shawarata ba a yanzu, tattalin arzikin zai yi kasa fiye da abin da muke fada.”

A baya mun ji cewaPrimate Elijah Ayodele, ya yi hasashen abubuwan da za su faru da wasu manyan mutane kamar su Shugaban kasa Bola Tinubu, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da shugaban IPOB a 2024.

A cewar Ayodele, Allah ya nuna masa wasu abubuwa, da ke nuna cewa za a samu sabanin siyasa da zai kai ga barkewar rikici tsakanin Shugaban kasa Bola Tinubu da Nyesom Wike.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN