Lamarin ya faru ne a yau Litinin 4 ga watan Disamba a cikin asibitin kwararru da ke birnin Benin City a jihar, Legit ta tattaro.
Hargitsin ya fara ne yayin da jami’an DSS su ka kawo dan uwansu zuwa asibitin bayan ya fadi yayin wani taro wanda ma’akatan asibitin ba su musu tarba mai kyau ba.
The Nation ta tattaro cewa an samu daidaito bayan shiga lamarin da shugaban masu tsaron gidan gwamnati ya yi da kuma hukumar ‘yan sanda.
Wani daga cikin jami’an DSS ya bayyana yadda abin ya faru inda ya ce ba su samu tarba mai kyau a asibitin ba inda su ke bukatar kulawar gaggawa.
Daraktan asibitin, Dakta David Odiko ya ce jami’an DSS sun ki amincewa sun kawo shi matacce amma likita ya kula da shi har ya fada musu cewa ya mutu.
From ISYAKU.COM