Zaben Imo 2023: Fada ya barke yayin da INEC ta fara tattara sakamakon zabe


An samu hatsaniya a makarantar firamare ta garin Umuodu, Ezinihitte Mbieri, a karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo, wurin da ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da ake yi, yayin da wasu ‘yan siyasa suka yi awon gaba da jami’an zabe da takardun rubuta sakamakon zabe. Legit Hausa ya wallafa.

Wakilinmu wanda ya bi diddigin lamarin, ya lura cewa an fara samun matsala ne bayan da jami’an hukumar zabe ta INEC, suka sanar da kuri'un da kowace jam’iyya ta samu a rumfar 015 da 016, ba tare da sun shigar da hakan a cikin takardar sakamakon zaben ba.

A rumfar 016, jami'in INEC ya fadi sakamako kamar haka:

LP - 19

APC - 21

PDP - 16

ADP - 2

AA - 1

Sai dai an bukaci jami’an da kada su shigar da sakamakon zaben a cikin takardar tattara sakamakon zaben, suka ki, lamarin da ya haifar da fada tsakanin jam’iyyun APC, LP, da PDP.

A yayin da ake ci gaba da hatsaniyar, wasu ‘yan siyasa da ake kyautata zaton ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki ne a jihar, su ka yi awon gaba da jami’an hukumar zaben tare da kayan zaben da suka hada da takardar rubuta sakamakon zaben.

Cikakken labarin yana zuwa...


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN