Jami’an soji sun kashe wani mutum da aka ce yana goyon bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Kogi, Umoru Agabidu.
An bayyana cewa wanda ake zargin ya je rumfar zabe da ke Agala Ogane, Anyigba a karamar hukumar Dekina a jihar, domin kwace akwatin zabe yayin da ake ci gaba da kada kuri’a.
An yi zargin cewa jami’an soji da ke bakin aiki a sashin zabe ne suka harbe Umoru da misalin karfe 10:00 na safe.
A cewar wani shaidan gani da ido, Umoru ya damke na’urar BVAS da karfin tsiya sannan ya farfasa ta a kasa a kokarinsa na daina kada kuri’a a rumfar zabe.
Wata majiya ta ruwaito cewa, “Wannan ya faru ne a sashin zabe da nuke zaune. Sun gargade shi da kada ya dauki akwatin zabe amma bai saurare su ba. Sojoji ne suka harbe shi a lokacin da yake shirin tafiya da akwatin zabe.”