Akalla mata 1,000 daga kauyuka 20 a karamar hukumar Awka ta Kudu, jihar Anambra suka fito kan tituna tsirara suna zanga-zanga. Legit Hausa ya wallafa.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba, inda rahotanni suka bayyana cewa, matan na zanga-zangar ne kan kashe-kashen da ake yi a garuruwansu.
Duk da suna tsirara ba su damu ba, haka suka karade babban birnin jihar dauke da kwalaye masu rubutu, suna zargin wasu jami'an 'yan sanda da hannu a cin hanci da rashawa, rahoton da jaridar The Nation ta fitar.
An gansu dauke da akwatin gawa da ke nuna alamar binne jami'an 'yan sandan da suke zargi, tare da ba hukumar wa'adin kwanaki 7 ta kori jami'an.
An rubuta a jikin wasu kwalayen cewa: "Matsafa na kashe mutanen mu", "A kori bara gurbi a aikin 'yan sanda", “DC na haifar da matsalar tsaro a Awuka”, “A kawo karshen cin hanci da rashawa”, da dai sauransu.
Da yake magana a madadin masu zanga-zangar, Richard Onuorah, ya ce daga yanzu jama'arsu ba za su amince da kashe-kashe da nakasa mutanensu ba.
Shima da yake jawabi, shugaban kungiyar garin na Ezinano, Tochukwu Nwokoye, ya bayyana fatansa na cewa zanga-zangar zata kawo karshen tashe tashen hankula a Awka.
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa tun a watan Satumba matan suka yi barazanar yin zanga-zangar tsirara ma damar ba a daina kashe mutanensu ba
From ISYAKU.COM