Inna lillahi, Jami’an shige da fice sun mutu, wasu sun jikkata a wani hatsarin mota a Kano (bidiyo)


Jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS) da dama ne aka tabbatar sun mutu yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Kano.


 Mummunan lamarin da ya afku a kusa da garin Kura da ke kan titin Kano/Zaria a yammacin ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, 2023, ya shafi wata motar bas kirar Nissan mai dauke da fasinjoji 18, wata motar hukumar shige da fice.


 Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Kano, Abdullahi Labaran ya ce lamarin da ya rutsa da jami’an hukumar tara ya faru ne sakamakon fashewar taya.


 Labaran ya tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu nan take yayin da aka garzaya da wasu mutane bakwai da suka jikkata zuwa asibiti.


 Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa wadanda hatsarin ya rutsa da su tare da wasu jami’an tsaro na cikin wata doguwar ayarin motocin da ke kan hanyar zuwa Abuja bayan sun halarci bikin faretin kammal samun horo da aka gudanar a ranar Asabar a Kano, lokacin da hatsarin ya afku.


 An kai gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka samu munanan raunuka zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano.


 Wani faifan bidiyo da aka gani a yanar gizo ya nuna gawarwakin jami’an shige da fice da abin ya shafa a kan hanya yayin da aka ga masu tausayawa suna kokarin farfado da wasu daga cikinsu.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN