Wata sanarwa da daya daga cikin ‘ya’yansa, Mohammad Usman ya fitar, ta ce jarumin ya rasu ne a safiyar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba a wani asibiti mai zaman kansa da ke jihar Kaduna bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Marigayi jarumin Kannywood ya yi aikin sojan Najeriya kafin ya yi ritaya daga bisani ya yi aiki a gidan rediyon tarayyar Najeriya FRCN da ke Kaduna.
Yana da shekaru 84 a duniya. Ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya goma sha biyu.
Za'ayi Sallar Jana'izarsa a masallacin Kabala Costain dake cikin babban birnin Kaduna, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.