Hatsabibin dan daba da ake nema ya mika kansa ga ‘yan sanda a Kano


Wani dan daba mai suna Hantar Daba da ‘yan sanda suka bayyana suna nema ruwa a jallo a jihar Kano ya mika kansa ga hukumar.


 Idan dai za a iya tunawa, rundunar ta bayyana cewa, Hantar Daba da wasu manyan ‘yan daba guda biyu, Abba Burakita da Nasiru Abdullahi, wanda aka fi sani da Chile Mai Doki, ana nemansu ruwa a jallo tare da sanya wa kowannen su kyautar N500,000 idan aka bayar da labarin inda za a kama su.


 Burakita da Chile Mai Daba sun mika kansu ga ‘yan sanda tare da mabiyansu.


 Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, 2023, ya ce Hanta Daba ya mika kansa a ranar Litinin din da ta gabata kuma ya bukaci kasancewa cikin shirin yin afuwa na gwamnatin jihar Kano ke yi.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN