An shiga dimuwa da mamaki yayin da Hukumomin Saudiyya suka soke bizar dukkan fasinjoji 264 da aka dako daga Kano da Legas a ranar Lahadi.
Jami'an na Saudiyya sun dage cewa jirgin ya mayar da su Najeriya inda ya dako su. Legit Hausa ya wallafa.
Jirgin ya tashi ne daga filin jirage na Murtala Mohammed, Legas ta filin Malam Aminu Kano da ke Kano a daren ranar Lahadi ya kuma dira filin Sarki Abdul-Aziz, Jeddah a Saudiyya, rahoton Daily Trust.
Amma abin mamaki ga ma'aikatan jirgin, Hukumomin Saudiyya suka sanar cewa an soke bizar dukkan fasinjojin.
Hakan na zuwa ne duk da cewa dukkan fasinjojin an musu bincike na APIS a Najeriya kafin su taso kuma jami'an Saudiyya suna sa ido a kai.