Bidiyon Gwamnan Kebbi yana ba jami'an tsaro kudi a wajen aiki ya ja cece-kuce saboda rashin sirri (Bidiyo)


Wani faifen bidiyo da ya nuna Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris yana ba jami'an tsaro kyautar kudi a wajen aiki ya ja cece-kuce a jihar Kebbi.


Bidiyon wanda wani hadimin Gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook yan kwanaki da suka gabata, ya sa jama'a na ta tofa albarkacin bakinsu kan inganci ko akasin yin haka da Gwamna ya yi.


Lamari da aka tallata a shafin sada zumunta marmakin sirri, duba da lamari ne da ya shafi jami'an tsaro, wanda ke bukatar martabawa da mutuntawa duk da yake Gwamnan ya yi da kyakkyawar manufa.


Wani abun mamaki shine yadda aka gan dogarin Gwamnan na hukumar DSS yana tsaye yana kallo, amma bai hana mai daukan didiyon daukar lokacin da Gwamna zai mika wa jami'an kudin ba. Wanda masana ke zargin cewa huruminsa ne ya dau mataki cikin hikima da ya dace nan take. 


Seniora Files wacce ke tattata bayanai, da shafin labarai na yanar gizo isyaku.com sun tattaro cewa wannan lamari ya zama abin gulma yanzu haka tsakanin jama'ar jihar Kebbi wanda basa tattaunawa a yanar gizo don dalilai na kariyar kai. Lamari da zai iya haifar da illar martaba ga Gwamnatin jihar Kebbi ta karkashin kasa.


Sai dai ko a lokacin yakin neman zaben Gwamna, wani faifen bidiyo ya zagaya matuka, inda aka gan Dan takarar Gwamna, kuma zababben Gwamna a yanzu, yana yi wa iyalan jami'an tsaro a barikinsu alkawarin makuddan kudade har da katon Sa don su taya shi murna idan ya ci zabe. Lamari da masana ke ganin bai kamata a saki wannan irin bidiyo a yanar gizo ba, ko a wane irin hali ne ko manufa.


Duk da yake a bayyane yake Gwamnan jihar Kebbi Dr Nasir Idris ya sha bayar da kyautar makuddan kudade ga Jama'a bisa amana da kyakkyawar zuciya. Sai dai masana harkar tsaro sun ce ba kowane yanayi na kyautar kudi ne za a dauka a watsa a yanar gizo ba, saboda taku, da dabarun tsaro a tsarin tafiyar da ingantaccen mulki ga al'umma.


Rashin sirri: Bidiyon Gwamnan Kebbi yana ba jami'an tsaro kudi a wajen aiki ya ja cece-kuce..Asalin bidiyo Zaidu Bala

Posted by ISYAKU.COM on Monday, November 13, 2023

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN