Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wata amarya ‘yar shekara 20 mai suna Amina Hassan da ke karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa bisa laifin kona gidan mijinta saboda ya ki sakin ta.
Wanda ake zargin ta yi aure da mijinta, Muhammed Auwal kimanin sati 5. Ta shaida wa ’yan sanda cewa ta kona gidan ne saboda kin amincewa da mijin nata ya yi na kawo karshen aurensu.
‘’Mun shirya cewa zai sake ni bayan auren. Na sadu da shi na roÆ™e shi ya sake ni, amma ya dage. Ya sauko a kaina ya fara dukana maimakon ya sake ni, sakamakon haka na fusata na kona gidan", ta ci gaba da cewa.
Mazauna unguwar sun ce kwanaki kadan kafin bikin auren, Amina ta shaida wa iyayenta cewa ba ta da sha’awar auren, amma iyayenta sun ce babu gudu babu ja da baya domin sun riga sun raba katin gayyatan autenta. Bayan an daura auren, sai amaryar ta nemi taimakon wani malamin tsibbu domin ya kawar da zuciyar mijinta daga gare ta ko kuma ya sa ya tsane ta don ya sake ta.
Bayan ya karbi kudi naira 12,000 na aikin daga wajenta, malamin tsibbun ya yi duk wani aikin da ya kamata ya yi, ya yi nasarar kawar da zuciyarta daga mijinta maimakon zuciyarsa daga gare ta kamar yadda suka amince. Ta koka da yadda malamin tsibbun ya koma Maiduguri a jihar Borno kuma yanzu ba a iya samun lambar wayarsa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, lSP Suleiman Nguroje, ya ce ‘yan sandan na ci gaba da gudanar da bincike.