Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta gaji manyan basussuka amma kuma ta gaji kadarori daga daga waÉ—anda suka gabace shi.
Tinubu wanda ya yi magana a daren ranar Litinin a birnin Makkah na Saudiyya, ya koka kan yadda Najeriya ke fama da matsanancin giɓi a bangaren tashoshin jirgin uwa da samar da wutar lantarki, da kuma ayyukan noma
Sai dai shugaban na Najeriya ya ce ba wani uzuri da zai nema, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Talata ta bayyana
“Akwai sassa da yawa cike da damar saka hannun jari ga masu saka hannun jari masu wayo. Samun kuÉ—i da tabbaci na iya zama cikas a wasu lokuta. Kuna iya shigowa wajen. Muna ganin ku a matsayin masu ba da taimako."
"Kun yi tarayya da mu a baya. Muna so mu haɓaka shi a yanzu kuma mu yi abubuwa da yawa tare da babban buri da hangen nesa mai haske."
A taron na Makkah, Shugaba Tinubu ya kuma cigaba da tattaunawa game da ayyukan samar da ababen more rayuwa na biliyoyin daloli daga bankin raya ƙasa na Musulunci don samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan more rayuwa da dama a matakin tarayya da na ƙananan hukumomi a Najeriya.
Wannan cigaban ya samo asali ne daga wata muhimmiyar tattaunawa kan saka hannun jari da aka yi tsakanin Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban bankin raya ƙasa na Musulunci, Dokta Mansur Muhtar.