Yanzu yanzu: Gobara ta tashi a hedikwatar Yan sandan...ta raunata mutane da dama...


Wata babbar gobara ta tashi a hedikwatar 'yan sanda a birnin Ismailia na kasar Masar a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, inda ta raunata akalla mutane 38 kafin a kashe ta, a cewar ma'aikatar lafiya.

 Kakakin 'yan sandan ya ce an yi wa wasu daga cikin wadanda suka jikkata magani a wurin, yayin da wasu kuma aka kai su asibiti.

 Ba a dai bayyana musabbabin tashin gobarar a ginin da ke Ismailia ba, in ji jami'ai.

 Akalla motocin daukar marasa lafiya 50 da jirage biyu ne aka aika zuwa wurin.

Daga cikin mutane 26 da suka samu raunuka wadanda aka kai su wani asibiti na yankin, 24 sun yi fama da “asphyxia" an yi wawasu mutum biyu magani sakamakon konewa, in ji ma’aikatar lafiya.  An yi wa wasu 12 magani a wurin.

 Ministan cikin gida Mahmoud Tawfik ya ba da umarnin gudanar da bincike kan musabbabin gobarar a ginin, in ji wata sanarwa da ma'aikatarsa ​​ta fitar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN