Harin na sama ya kuma lalata maboyar 'yan ta'addar, da gine-gine, da kuma maboyarsu.
Kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, 2 ga Oktoba.
Ya ce an far wa ‘yan ta’addan ne a wuraren da suke Tumbun Fulani da yankin Tumbun Shitu da ke gabar tafkin Chadi daga ranar 27 zuwa 30 ga watan Satumba.
Kakakin NAF ya ce hare-haren ta sama ya zama wajibi ne bayan da sojoji suka tabbatar da ayyukan ‘yan ta’addan “ya zama barazana ga tsarin soja da ‘yan Najeriya masu bin doka da oda da ke zaune a wuraren.”
Gabkwet ya ce: “A Tumbun Fulani, an ga ‘yan ta’adda suna loda jarkoki a cikin manyan motoci biyu da aka boye a karkashin bishiyoyi.
DAGA ISYAKU.COM