Wani Supritanda na Yan sanda Nahun Gwadi Eli ya rasu a dakinsa na otel dake Jos babban birnin jihar Filato.
An tsinci gawar jami’in ne a kasa a gefen gadonsa bayan da jami’an da abin ya shafa suka fasa dakin otal dinsa a ranar 23 ga Oktoba, 2023.
Har zuwa rasuwarsa, Eli shi ne Kwamandan A/O SWAT, Rundunar Jihar Filato.
A cewar majiyoyi, mutanen nasa sun shiga cikin damuwa bayan da suka yi ta kiran layin wayarsa ba tare da amsa ba.
’Yan sandan sun nufi dakinsa na otal inda suka yi ta kwankwasa sau da yawa, amma ba su samu amsa ba.
Sai da suka bude kofar dakin otal suka same shi ya mutu.
An dauke gawarsa zuwa dakin ajiye gawa na asibitin Jos domin gudanar da bincike.