Ƙungiyoyin kwadago sun janye yajin aiki na kwanaki 30: Cikakkun bayanai kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin FG da shugabannin kwadago


Daga karshe shugabannin kungiyoyin kwadago na kasa NLC da TUC sun janye tafiya yajin aikin sai baba ta gani da suka shirya zuwa, wanda ya kamata ya fara daga ranar Talata, 3 ga watan Oktoba.

kungiyoyin kwadagon sun sanar da soke tafiya yajin aikin ne a cikin wata sanarwa da suka saki bayan ganawarsu da wakilan gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.

Ga jerin yarjejeniyar da aka cimmawa tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kwadago bayan tattaunawarsu don hana tafiya yajin aiki.

1. Gwamnatin tarayya ta amince da biyan 35,000 ga dukkan ma'aikatan gwamnati daga watan Satumba zuwa lokacin da ake sa ran sanya hannu a sabon mafi karancin albashi na kasa.

2. Za a kaddamar da kwamitin tsara mafi karancin albashi cikin wata daya daga ranar da a ka kulla wannan yarjejeniya.

3. Gwamnatin tarayya ta janye harajin VAT a man Dizal na tsawon wata shida farawa daga watan Oktoban 2023.

4. Gwamnatin tarayya ta amince da naira biliyan 100 don gaggauta samar da motoci masu amfani da gas don saukaka matsalolin sufuri.

5. Gwamnatin Tarayya na shirin aiwatar da matakai daban-daban na karfafa haraji ga kamfanoni masu zaman kansu da sauran jama'a.

6. Dangane da rigingimun shugabanci da ya dabaibaye kungiyar NURTW da kuma zargin haramtawa RTEAN, Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen tafiyar da al’amuran Ma’aikata daidai da Yarjejeniyar ILO da Dokar Kwadago ta Najeriya. Ana sa ran za a warware rikicin da ke gudana nan da 13 ga Oktoba.

7. An mika batun albashin da ma'aikatan jami'o'in tarayya ke bi ga ma'aikatar kwadago da daukar ma'aikata don ci gaba da tattaunawa.

8. Gwamnatin tarayya ta yanke shawarar rabawa gidaje miliyan 15 tallafin N25,000 na tsawon wata uku, fara daga watan Oktoban 2023.

9. Gwamnatin tarayya za ta kara kaimi wajen rabon tallafin takin zamani ga manoma a fadin kasar.

10. Ya kamata gwamnatin tarayya ta bukaci gwamnonin jiha ta majalisar tattalin arziki na kasa da kungiyar gwamnoni da su aiwatar da karin albashin ga ma'aikatansu. Haka kuma ya kamata a yi hakan ga ma'aikatan karamar hukuma da kamfanoni masu zaman kansu.

11. Gwamnatin tarayya ta himmatu wajen samar da kudade ga masu kananan sana'o'i kamar yadda shugaban kasar ya sanar a jawabinsa na ranar 1 ga watan Agusta.

12. Za a gudanar da ziyarar hadin gwiwa a matatun mai domin tabbatar da matsayin gyaransu.

13. Dukkan bangarorin sun kuduri aniyar ci gaba da bin ka'idojin sulhu a duk ayyukanmu na gaba.

14. Kungiyoyin NLC da TUC sun amince da dakatar da yajin aikin sai baba ta gani da suke shirin farawa a ranar Talata, 3 ga watan Oktoban 2023 na tsawon kwanaki 30.

15. Za a gabatar da takardar yarjejeniya da bangarorin suka sa hannu ga kotun da ta dace cikin mako guda a matsayin hukuncin da gwamnatin tarayya ta amince da shi.

Rahotun legit Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN