Mutane hudu daga cikin iyalin gidan mutane biyar a jihar Taraba sun mutu bayan da wutar lantarki ta kama su a unguwar Dinyavo da ke Jalingo, babban birnin jihar a ranar Litinin 2 ga watan Oktoba.
Mahaifi da mahaifiyarsa da yara biyu suna cikin gidansu lokacin da ibtila'in wutar lantarkin ta afku.
Mazauna yankin sun ce suna zargin cewa wutar lantarkin ta faru ne sakamakon karfin wutar lantarki da aka samu daga na’urar sadar da wutan lantarki ta kasa ya haddasa lamarin.
‘’Da safiyar yau, sai ga wani fashewa daga na’urar taranfoma. Kowa ya fita da gudu hayaki ya biyo baya. Bayan 'yan dakiku, kowa ya fara ihu, kafin mu ankara sai ga wasu gidaje da yawa sun cika da hayaki. Na yi iya kokarina na ceto su, duk abin ya ci tura, domin sun kulle kansu, amma da muka yi nasarar karya kofar, sai muka gane cewa wutar lantarki ta kama su, su ma makwabtan sun firgita, suka garzaya da su. asibiti.” Inji wani ganau
An ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawarwaki.
DAGA ISYAKU.COM