Bola Tinubu ya soke nadin da ya yi wa Engr mai shekaru 24 a duniya Imam Kashim Imam a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA).
Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba.
An sanar da nadin Imam ne a ranar Juma'a, 13 ga Oktoba. Shugaban ya nada dan shekaru 24 "don sabunta wa'adin shekaru hudu (4), daidai da Sashe na 2 (3) na Dokar Gyaran FERMA, 2007".
Nadin ya haifar da damuwa, mutane da yawa sun ce bai da kwarewar da ake bukata don aikin.
Bayan martanin, Ngelale ya ce an janye nadin ba tare da bata lokaci ba.
Duk da cewa babu wani dalili da fadar shugaban kasa ta bayar na daukar wannan mataki, Ngelale ya ce duk sauran nade-naden da aka yi a hukumar da hukumar gudanarwa ta FERMA ba ta shafi wannan umarnin ba.
From ISYAKU.COM