Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ribas sun cafke wata uwar ‘ya’ya biyu da ta watsa wa mijinta Acid a fuska a kan rabon Naira 15,000 da aka biya kowane iyali a unguwar Nchia da ke karamar hukumar Eleme.
Mummunan lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba. PM News ya rahoto.
Rahotanni sun bayyana cewa, matar ta samu rashin jituwa da mijin ta wanda ta yi zargin ya kwace kason N15,000 da aka baiwa iyalan da kamfanoni na kasa da kasa da ke yankin suka ba al'ummar .
Ta ce mijin ya ki biyan ta kasonta na ‘ya’ya biyu daga cikin kudin.
A fusace matar ta zuba wa mijin nata acid sannan ta kwace masa katin ATM din sa ta yi yunkurin tserewa.
Sakamakon haka mijin ya yi kururuwa wanda ya ja hankalin yan banga. Ganin yan banga sun biyo ta, sai ta gudu ta koma gida ta boye a cikin silin.
Daga bisani yan banga sun sauko da ita daga silin na gidan, suka mika ta ga yan sandan garin Eleme dake karamar hukumar Eleme don ci gaba da bincike, yayin da aka garzaya da mijin zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin neman kulawar gaggawa.
DAGA ISYAKU.COM