![]() |
Illustrative picture |
Yayin da ‘yan Najeriya ke fafutukar tinkarar mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki sakamakon cire tallafin man fetur, majalisar wakilai ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen rabon motocin hukuma ga ‘yan majalisar wakilai ta 10.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Akin Rotimi, ya ce hukumar na cikin shirin sayo da raba motocin ga mambobin. Daily trust ta rahoto.
Wani bangare na sanarwa ya ce:
“Ba kawai yan Majalisar ba, domin jami’an gwamnati da ba a zaba a bangaren zartarwa na gwamnati ba tun daga matakin Mataimakin Darakta zuwa sama, a mafi yawan lokuta, suna da motocin hukuma a ofisoshinsu.
Yana da mahimmanci a yi bayani. Motocin da za’a ware wa ofisoshin ‘yan Majalisa motoci ne da aka tanada don ayyukan sa ido wajen gudanar da ayyukansu a kwamitoci. Ba motocin sirri ba ne da aka baiwa mambobi masu daraja.
A tsawon lokacin Majalisa ta 10 (2023 – 2027), motocin za su ci gaba da zama mallakin Majalisar Dokoki ta kasa.
A karshen wa’adin majalisa ta 10 a shekarar 2027, idan har yanzu tsarin tafiyar da kadarorin gwamnati na nan daram yadda yake a yanzu, ‘yan majalisar za su iya samun zabin biyan kudin motocin a asusun gwamnati kafin su zama nasu. , in ba haka ba, motocin za su ci gaba da zama mallakin Majalisar Dokoki ta Kasa". Ya ce.
From ISYAKU.COM