An banka wa Majalisar dokokin jiha wuta bayan yunkurin tsige Gwamnan PDP


A daren ranar 29 ga watan Oktoba ne wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka bankawa majalisar dokokin jihar Ribas wuta sakamakon yunkurin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da shugaban majalisar, Edison Ehie.


 Wasu ‘yan baranda a cikin wata farar motar Hilux sun mamaye harabar majalisar da misalin karfe 9 na dare, inda suka kwance wa jami’an tsaron da ke bakin aiki makamai kuma suka tafka barnar.


 An tattaro cewa lamarin ya faru ne a harabar majalisar da ke daura da hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar da ke kan titin Moscow a Fatakwal.


 Ana zargin ‘yan majalisar sun kammala shirin tsige Fubara da Ehie a yau 30 ga watan Oktoba inda suka koma zama bayan wasu batutuwa da ba a bayyana ba.


 Sama da manyan motocin tsaro 17 da kuma motocin daukar kaya guda hudu (APC) tare da jami'an tsaron tarayya sama da 50 ne aka jibge a wurin.  Akwai rade-radin cewa akwai rashin jituwa tsakanin gwamnan da magabacinsa Nyesom Wike, wanda yanzu ya zama ministan babban birnin tarayya.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN