Zanga-zangar MohBad a ranar Talata ta yi sanadin toshe manyan tituna a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.
A cikin wani faifan bidiyo da Jaridar The Nation ta gani, masu zanga-zangar a daruruwansu sun fito kan tituna sanye da bakaken kaya don girmama marigayin mawakin yayin da suke rera wakar Justice for Mohbad.
Wasu masu É—auke da kwalaye da rubutu kamar "Adalci ga Mohbad".
An kuma lura da kasancewar jami'an tsaro a yayin da matasan ke tattakin
Published by isyaku.com