Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe diyar wani dan sanda mai shekaru goma sha daya a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
An kashe yarinyar mai suna Hauwa’u Lawali, bayan an sace ta daga gidan mahaifinta da ke unguwar Saminaka a Gusau.
An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan dan sandan da ke aiki da rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a daren ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba, 2023, inda suka yi awon gaba da yarinyar.
A cewar wani rahoton gidan talabijin na TVC, masu garkuwa da mutanen sun harbe yarinyar ne a ranar Litinin din da ta gabata, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa daji bayan da suka lura cewa jami'an tsaro na bin su.
Hukumomin ‘yan sanda a Zamfara sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce har yanzu jami'an tsaro suna cikin daji suna bin ‘yan ta’addan.
Published by isyaku.com