Tsakanin tsohon Ministan Sharia Abubakar Malami SAN, da Gwamna Nasir Idris a jihar Kebbi, bayanai sun fito


Sakamakon bincike ya tabbatar cewa babu wata damuwa balle baraka tsakanin tsohon Ministan Sharia na Najeriya Abubakar Malami SAN, da Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris.

Biyo bayan sakamakon bincike da Seniora Files ta gudanar tare da hadin gwiwa da shafin labarai na isyaku.com dangane da jita-jita dake ke yawatawa musamman a garin Birnin kebbi.


Sakamakon binciken ya bayyana cewa kagaggen lamari ne kawai kuma babu wata damuwa, balle baraka tsakanin Abubakar Malami  SAN da Gwamna Nasir Idris.


Binciken ya samo daga madogara mai karfi, cewa lamarin ba gaskiya bane. Kazalika sakamakon rahotun ya samo cewa har yau da gobe, Abubakar Malami SAN jigo ne mai farar aniya ga ci gaban jjihar Kebbi da jam'iyar APC a jihar da fadin kasar man.


Martabar Abubaar Malami da jama'a basu sani ba


Rahotun Seniora Files da isyaku.com ya gano cewa, tun bayan gagarumin gudunmuwa da Abubakar Malami SAN ya bayar a zabukan 2023 a matakin jiha da tarayyar Najeriya. Bayan nassarori da jam'iyar APC ta samu, Malami ya ci gaba da harkokin gabansa.


Tun farko Abubakar Malami SAN, yana da abin yi, na hidimar rayuwa da tallafa wa jama'a, lamari da ya sa ya fuskanci hatkokin gabansa domin ya bar Gwamna Nasir Idris ya yi aikinsa ba tare da an yi masa katsalandan ba.


Inda matsalar ta samo asali


Bayan an kammala zaben 2023, akwai zargin cewa wasu yan siyasa sun yi kane-kane a fadar Gwamnatin jihar Kebbi, ba safe ba rana balle dare. Sun matse wa Gwamna. Sai dai Seniora Files da isyaku.com sun gano cewa Abubakar Malami SAN ya fuskanci hatkokin gaban shi ne kawai, kuma ba acikin garin Birnin kebbi kawai ba.


Yadda Abubakar Malami SAN ya sama wa matasa 260 aikin yi a Kebbi bayan ya sauka daga Minista.



Bayan saukansa daga mukamin Minista, Abubaar Malami SAN, ya sama wa matasan jihar Kebbi 260 aikin yi ta hanyar buda sabon kampani, irinsa na farko a tarihin jihar Kebbi, inda aka horar da matasa kan harkar tsaro karkashin Rayhaan Alert Security, bayan dimbin ayyuka, da damarmaki da Abubakar Malami SAN ya sama wa al'ummar jihar Kebbi lokacin da yake Ministan Sharia.

Bayanai sun nuna Abubakar Malami SAN, ya yi wannan ne domin kara tallafawa Gwamnatin jihar Kebbi bisa mamufarta na sama wa matasan jijar aikin yi.


NSCDC trains 260 1st indigenous private security Rayhaan Alert Security corps in Kebbi

Za mu ci gaba da yardar Allah....

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN