Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Gabon sun sake daukar wani muhimmin mataki



Sojojin kasar Gabon sun fadi a ranar Asabar cewa za su sake bude iyakokin kasar, wadanda suka rufe sakamakon juyin mulkin da suka yi na hambarar da tsohon shugaban kasar Ali Bongo, Channels Tv ta ruwaito. 

$ads={1}

Mai magana da yawun shugabannin mulkin sojan Gabon ne ya fadi hakan a gidan talabijin na kasar cewa, sun yanke shawarar ne nan da nan don sake bude iyakokin kasa, ruwa da iska tun daga wannan Asabar din. Legit ya wallafa.

Idan baku manta ba, wasu gungun sojojin kasar Gabon su 12 sun sanar a ranar Laraba cewa sun rufe iyakokin kasar har zuwa wani lokacin a wata sanarwar da aka watsa a tashar talabijin ta Gabon 24.

Janar Brice Oligui Nguema, shugaban rundunar tsaron shugaban kasar a ranar Laraba ne ya jagoranci jami'ansa a juyin mulkin da suka yi wa shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, dan gidan da ya shafe shekaru 55 yana mulki.

$ads={2}

Korar tasa ta zo ne bayan da aka ayyana Bongo mai shekaru 64 a matsayin wanda ya sake lashe zaben shugaban kasa a karshen mako - sakamakon da 'yan adawa suka yi zargin an yi magudi.

Shugabannin juyin mulkin sun ce sun rusa hukumomin kasar tare da soke sakamakon zaben da kuma rufe kan iyakokin kasar, France24 ta ruwaito.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN