Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto ta yi watsi da karar da Sa’idu Umar dan takarar jam’iyyar PDP ya shigar yana kalubalantar nasarar Ahmed Aliyu a matsayin gwamnan Sokoto a zaben ranar 18 ga watan Maris.
Sa’idu Umar ya tunkari kotun don yin watsi da nasarar Aliyu. The Nation ta rahoto.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Aliyu a matsayin wanda ya lashe zaben, amma Umar ya fafata da Aliyu inda ya ce mataimakin Aliyu Idris Gobir bai cancanta ba, kuma an tafka magudi a zaben.