Yero ya bayar da bayyana matakin ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Satumba kuma zuwa ga shugaban PDP na gundumar Kaura a karamar hukumar Zariya ta jihar.
Ya ce;
“Tare da godiya ga Allah Madaukakin Sarki, na rubuta ne domin mika sakon gaisuwata tare da sanar da ku shawarar da na yanke na ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
"Saboda haka, na gabatar da murabus na a matsayin dan jam'iyyar PDP daga ranar 30 ga watan Satumba, 2023. A cikin wannan, na dawo da katin zamana dan jam'iyya."
Yero, wanda kuma shi ne Dallatun Zazzau, ya taba zama mataimakin gwamna ga marigayi Gwamna Patrick Yakowa wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama. Ya zama Gwamnan Jihar Kaduna tsakanin 15 ga Disamba 2012 zuwa 29 ga Mayu, 2015.
Published by isyaku.com