An tsinci gawar wani matashi dan shekara 27 ma'abuci amfani da kafafen sada zumunta, Yusuf Mubarak wanda aka bayyana bacewarsa a jihar Kwara.
An ce an yi wa Mubarak ganin karshe ne a unguwar Sakatariyar Tarayya, kan titin Tarayya da ke Birnin Ilorin, da misalin karfe 9:40 na dare. a ranar Laraba, 13 ga Satumba, 2023.
Tun daga wannan lokacin, ba a sake jin duriyar dalibin Jami’ar Jihar Nasarawa ba. Sai dai an tsinci gawarsa a unguwar Unity Road da ke cikin birnin Ilorin a ranar Asabar, 16 ga watan Satumba.
Wani dan jarida mai suna Saeed Tijjani ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya wallafa a Facebook.
“Ya ku ‘yan uwa da masoyan Yusuf Mubaraq, muna bakin cikin sanar da tabbatar da rasuwar dan uwanmu da aka bayyana bacewarsa jiya. Allah Ya karbi komawarsa gareshi, Ya gafarta masa zunubansa, Ya saka masa da Aljannah, kuma ya dawwama da dukkan abin da ya bari.” Inji shi.
Da yake mayar da martani game da faruwar lamarin, Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya umurci hukumomin tsaro da su gano bakin zaren lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Published by isyaku.com