Ma’aikatar lafiya ta jihar Neja ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu guda biyar saboda rashin cancantar ma’aikata da kuma rashin sabunta rajistar wuraren aikinsu na shekara ta 2023.
Cibiyoyin biyar da abin ya shafa sun hada da Prince Clinic a Tunga, Union Diagnostic a Minna, Triple Medical Diagnostic a Bosso, Chall Dental a Minna, da Daza Primary Healthcare a Beji.
An rufe asibitocin ne a lokacin wani binciken bazata ga cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu guda 40 a kananan hukumomin Bosso da Chanchanga da sashen sa ido na ma’aikatar lafiya ta gudanar.
Mataimakin shugaban sashin kula da lafiya wanda kuma shine mataimakin darakta a sashen kula da lafiya da horaswa, Usman Abubakar Bosso ya bayyana cewa asibitin da abin ya shafa basu yi rajista da ma’aikatar lafiya ba kuma ma’aikatar ba ta da bayanansu.
Ya kuma ce an gargadi wasu asibitocin da dama kan rashin tsaftar muhalli a lokacin atisayen.
Boss ya ce: “Wannan ya nuna cewa muna da ayyuka da yawa da aka rage mana. Galibin wadannan asibitocin hatsari ne ga rayuwar marasa lafiya. Daga yanzu, za mu fara irin wannan ziyarce-ziyarcen bazata a wurare masu zaman kansu don daukaka matsayin kiwon lafiya."
Published by isyaku.com