Shahararren malamin addinin Muslunci, Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya. Legit Hausa ya wallafa.
Allah ya karbi rayuwar Giro a yammacin yau Laraba 6 ga watan Satumba.
Giro kamar yadda Sheikh Kabiru Gombe ya wallafa a shafinsa na Facebook ya rasu bayan 'yar gajeriyar jinya a Birnin Kebbi.
Kabiru Gombe ya ce za a sallaci mamacin a gobe Alhamis 7 ga watan Satumba.
Published by isyaku.com