Kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta yi fatali da korafin jam'iyyar Labour kan safarar miyagun kwayoyi da ake kan Shugaba Tinubu. Legit ya wallafa.
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi na kalubalantar zaben da aka gudanar saboda tafka magudi.
Har ila yau, Peter Obi ya gaza kawo hujjoji kan cewa an taba kama Bola Tinubu a Amurka kan zargin safarar miyagun kwayoyi.
Gamayyar lauyoyi biyar da Mai Shari'a Haruna Tsammani ke jagoranta shi ya yi fatali da karar, cewar Channels TV.
Ya ce babu wata hujja da dan takarar da jamiyyarsa su ka kawo da ta ke tabbatar da kama Tinubu kan zargin safarar kwayoyi a Amurka.
Published by isyaku.com