Illustrative picture |
Akalla dan sanda daya da ke aiki da ofishin ‘yan sanda na yankin Iponri ya rasa ransa bayan da wasu Yan acaba suka kai musu hari a unguwar Ijora Olopa da ke jihar Legas a ranar Juma’a 12 ga watan Agusta.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an sun je yankin ne domin aiwatar da dokar takaita zirga-zirgar ‘yan Okada da gwamnatin jihar Legas ta yi a lokacin da ‘yan Okada suka kai musu hari da muggan makamai, kamar kwalabe, kulake, da laya. Maharan sun far wa ‘yan sandan tare da kokarin kona motar ‘yan sandan da ke aiki amma rundunar ‘yan sandan Rapid Response Squad da sauran jami’an ‘yan sanda da aka tura wurin da lamarin ya faru suka hana su. .
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LIB, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas (PPRO) SP Benjamin Hundeyin ya ce daya daga cikin ‘yan sandan biyu da suka samu munanan raunuka a harin ya mutu daga baya.
“’Yan sandan sun je yankin ne domin aiwatar da dokar hana Okada da gwamnatin jihar Legas ta yi a lokacin da aka kai wa ‘yan sandan hari.
An kama wasu daga cikin Yan Okada kuma an daidaita zaman lafiya a wurin.” Yace
Published by isyaku.com