Wasu mazauna jihar Kano a safiyar ranar Asabar, 12 ga watan Agusta, sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da shirin amfani da karfin soji da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ke shirin yi domin warware rikicin juyin mulkin Nijar.
Idan za a iya tunawa, a wani taro a Abuja a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, shugabannin ECOWAS sun umurci sojojin kasashen kungiyar da su kasance cikin shirin maido da mulkin dimokuradiyya a a Nijar.
Masu zanga-zangar sun yi adawa da wannan shiri. Sun dauki alluna daban-daban yayin da suke rera wakoki.
“Yan Najeriya ’yan uwanmu ne, ’yan Nijar kuma danginmu ne. Nijar tamu ce, ba ma son yaki, yaki da Nijar zalunci ne, makirci ne na sojojin kasashen yamma''
Masu zanga-zangar sun kuma nuna tutocin Najeriya da Nijar, suna rera wakokin adawa da yaki.
Published by isyaku.com