An kwashi yan kallo a bikin cikar jihar Edo shekaru 32 da kafuwa, wanda aka gudanar a dakin taro na New Festival, dake gidan gwamnati, a birnin Benin, jihar Edo, lokacin da wani jami'in tsaron gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya hana mataimakinsa Philip Shaibu isa wajensa a dakin bikin.
Hotunan da aka yada ta yanar gizo sun nuna wani jami'in tsaro ya hana Shaibu zuwa ganawa da Obaseki a yayin taron.
Hakan dai na zuwa ne bayan shafe makonni ana takaddama tsakanin gwamnan da mataimakinsa. Mataimakin dai ya garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ya samu umarnin dakatar da gwamnan da majalisar dokokin jihar daga yunkurin tsige shi.
Published by isyaku.com