Talakawa da aka ce sun fusata saboda wahalhalun da kasar ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi sun fasa Ma'ajiyar abinci na Gwamnatin jihar Bayelsa da ke kan titin Isaac Boro Express suka yi awon gaba da kayan abinci da ke ciki.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Bayelsa (BYSEMA) ta ce kayayyakin abincin da aka kwashe ba su da amfani ga dan Adam domin an ajiye su ne a lokacin ambaliyar ruwa ta shekarar 2022 a jihar.
Gwamnatin tarayya ta sanar da ware Naira biliyan 5 a matsayin tallafi ga jihohi domin rabawa ‘yan Najeriya.
Published by isyaku.com