Mai ba wa Gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkokin siyasa Alhaji Kabiru Sani (Giant) ya wakilci Gwamnan jihar Kebbi Dr. Nasir Idris a wajen ta'aziyyar.
Alhaji Kabiru ya roki Allah ya jikan mamatan ya yi masu rahama.
Ya kuma mika sakon kyautar Gwamna na Naira miliyan daya (N1m) ga iyalan mamatan.
Hakimin kauyen Kurya Alhaji Aliyu Musa ya gode wa gwamna Nasir bisa wannan ziyarar Ta'aziyya da kuma kyautar da aka yi wa iyalan mamatan. Ya kuma yaba wa Gwamna bisa yadda ya sa taimakon talaka gaba, duba da yadda ya raba wa jama'a taki kyauta kuma a daidai lokaci da ake bukata.
Tawagar ta kunshi Hon Umaru Sallah Sambawa, Dan Majalisar dokokin jihar Kebbi mai wakiltar Maiyama , Hon. Bello Abdullahi Mungadi, Alhaji Saidu Giwatazo, shugaba jam'iyar APC karamar hukumar Maiyama da sauran fitattun mutane da manyan yan siyasa.
Published by isyaku.com