Wani dan sanda mai ritaya mai shekaru 74 ya kashe kansa ta hanyar rataya a kauyen Mba, karamar hukumar Mbooni ta Gabas, gundumar Makueni.
An tsinci gawarsa rataye a jikin bishiyar mangwaro da ke gonarsa.
Shugaban yankin Kako/Waiya Patrick Ndiku ya ce matar marigayin ta shaida wa hukuma cewa tsohon ma’aikacin ya kira iyalansa da daddare ya sanar da su cewa zai tafi Mombasa ne domin duba harkokin kasuwancinsa kuma ya tafi da motar bas da karfe uku na safe.
Ya tashi da wuri ya shirya ya tafi Mombasa yayin da sauran 'yan uwa suke barci. Sun kadu bayan gano ya kashe kansa. Ndiku ra ce;
"Mutumin ya rataye kansa ne ta hanyar amfani da jaket din da yake sanye da shi amma ya tsage, sannan ya ci gaba da daure bel dinsa da rigar da yake sanye a cikin jakar ya kashe kansa."
Dan sandan mai ritaya bai bar wata takarda da ke bayanin dalilin da ya sa ya kashe rayuwarsa ba. Jami’an ‘yan sanda ne suka dauko gawarsa daga ofishin ‘yan sanda na Mbmbuni suka kai ta dakin gawarwaki ta Tawa domin adanawa.
Published by isyaku.com