Sanatocin Najeriya sun yi watsi da bukatar da Shugaba Bola Tinubu na neman izinin tura sojojin Najeriya zuwa jamhuriyar Nijar a matsayin wani bangare na muradin ECOWAS na maido da zababben Shugaban kasar Mohamed Bazoum.
An hambarar da Shugaba Bazoum ne a ranar 26 ga watan Yuli a wani juyin mulki karkashin jagorancin masu gadin fadar shugaban kasar, Vanguard ta tattaro. Legit ya wallafa.
Shugabannin ECOWAS a wani taro da suka yi a Abuja kwanaki hudu bayan haka sun ba wadanda suka yi juyin mulkin wa’adin kwanaki bakwai su maido da Bazoum kan kujerarsa.
An kakaba wa Nijar takunkumi
ECOWAS ta kuma kakaba takunkumi kan sabon mulkin na Nijar, inda ta umarci katse wutar lantarkin da Nijar ke mora daga Najeriya da kuma rufe iyakokinta.
Hakazalika, ECOWAS karkashin Shugaba Tinubu ta yi barazanar tura sojojinta zuwa Nijar domin kwace mulkin, wanda daga ciki har da sojojin Najeriya.
Sai dai, a zaman da suka yi a ranar Asabar 5 ga watan Agusta, Sanatocin sun yi watsi da bukatar shugaban kasar na tura sojojin Najeriya Nijar.
A cewar wani sanatan da ya halarci taron, Sanatoci sun amince da zartas da kudurin yin Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar din.
Published by isyaku.com