Shafin Comr Abba Sani Pantami NIG LTD, kamfanin labarai ne mai zamanshi dake da ragista karkashin hukumar CAC a Najeriya.
Ga wasu daga cikin ayyukan da ake gudanarwa a karkashin shafin kamfanin;
- Rubuce-rubucen wayar da kan al-umma.
- Rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabta.
- Tallace-Tallace.
- Rubutukan siyasa.
- Fadakarwa, Sharhi da Fashin Baki.
- Nishadi da Barkwanci.
- Rahotonni masu amfani ga al-umma.
Nan gaba kadan zai kara fadada wasu ayyukan, tare da sake fito da wasu sabbin tsare-tsare masu inganci na zamani.
Dubunnan daruruwan mutane a Najeriya ne suke matukar bibiyar shafin, domin samun ingantattun labarai a koda yaushe.
Mamallakin shafin Comr Abba Sani Pantami, ya kasance shahararran marubuci kuma dan jarida mai yada labarai a kafofin sada zumunta, da yayi kaurin suna a Najeriya.
Published by isyaku.com