Sanarwar manema labarai
Mai girma gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasiru Idris, Kauran Gwandu, ya sauke mai ba shi shawara na musamman kan harkokin matasa daga mukaminsa.
Korar S.A. ya biyo bayan wani posting na rashin mutunci da yayi akan matsayin sa na WhatsApp (Status)
Gwamnan wanda ya fusata da wannan mumunan lamari, ya ce Mataimakin ya tattake kyawawan dabi’u da zamantakewar al’ummar Kebbi, wanda galibinsu mabiya addinin Musulunci ne.
Kauran Gwandu ya sha alwashin cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci duk wani abu da zai zubar da mutuncin al’ummar jihar ba.
Gwamnan ya kuma gargadi sauran jami’an gwamnati da su guji yin irin wadannan munanan rubuce-rubuce a shafukansu na sada zumunta da sauran wuraren dandalin jama’a.
Sa hannu,
Ahmad Idris
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna
10/07/2023
Published by isyaku.com