Sanatoci za su binciki tsohuwar Gwamnatin Buhari bayan Majalisa ta yi muhimmin zargi


Majalisar dattawa ta ce za ta gudanar da bincike kan kwangilar aikin gas da aka ba kamfanin Acugas Limited a lokacin Muhammadu Buhari. Legit Hausa ya wallafa.

Abin da ya jawo maganar kuwa shi ne batun da Sanata Aniekan Bassey (PDP, Akwa Ibom) ya kawo a ranar Alhamis, Premium Times ta fitar da labarin.

Aniekan Bassey ya ce a shekarar 2017 ne kamfanin lantarki nan na NDPHC ya shiga yarjejeniyar Dala miliyan 10 da Acugas Limited domin samar da gas.

Lambar Zainab Ahmed za ta fito?

Wanda ta sa hannu domin a ba kamfanin Calabar Generation Company Limited gas din ita ce Zainab Ahmed, a lokacin ta na Ministar kudi da tattalin arziki.

Sanatan na Akwa Ibom ya ce makudan biliyoyin da aka batar ya jawo abin magana, kuma ana zargin akwai nuku-nuku wajen yadda aka biya kwangilar.

A dalilin haka, rahoton ya ce ‘dan majalisa ya bukaci idan an kafa kwamitin harkar lantarki, a bankado gaskiyar abubuwan da su ka faru wajen wannan aiki.

Za a so majalisa ta gayyaci duk wani ko hukuma da ke da hannu a kwangilar domin a ji ta bakinsu.

Ra'ayin sauran Sanatoci a Majalisa

Sanata mai wakiltar Kuros Riba ta tsakiya, Etang Williams ya nuna yana goyon bayan hakan. Daga baya Sanata Aminu Abass ya ce kudin ya yi yawa.

Bayan sauraron maganar irinsu Sanata Sampson Akpan (PDP, Akwa Ibom), Barau Jibrin da ya jagoranci zaman ya amince idan an kafa kwamiti, ayi bincike.

Jinginar da filayen jirgin sama

A zaman jiyan ne Aminiya ta rahoto cewa Abdulrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta kudu a majalisa ya kawo batun jinginar da wasu filin jiragen sama.

Sanatan kudancin Kano ya yi tir da yadda aka bada jinginar tashoshin Nnamdi Azikiwe da Aminu Kano a kudi kadan kafin Muhammdu Buhari ya bar ofis.

‘Dan Majalisar ya ce ba a bi ka’ida wajen bada jinginar ba, saboda haka ya bukaci a yi bincike. Nan take Majalisar Dattawan ta amince da maganar da ya kawo.

Gbenga Daniel ya tsaida cin fansho

Rahoton nan ya nuna sabon Sanatan Ogun ta gabas bai da niyyar hada albashin Majalisa da fanshon Gwamna kamar yadda wasu ‘yan siyasa su ke yi.

Gbenga Daniel ya aika takarda zuwa ga Gwamnansa, ya ce a tsaida kudin da ake biyan shi. Fanshonsa a wata ya kai N670,000, sai kuma albashin majalisa.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN