Sadaki ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya - Sarkin Musulmi


A ranar Juma'a, 12 ga watan Dhul Hijjah Hijira 1444, wacce ta yi daidai da 30 ga watan Yunin 2023, Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwar nisabin Zakkah, Sadaki da Diyyar rai. Legit ya wallafa.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal da gudanar da idin babbar Sallah da aka gudanar a ranar Laraba 10 ga watan Dhul Hijjah na wannan shekarar.

A sanarwar da sarkin Musulmin ya fitar, wacce hukumar kula da ganin jinjirin wata ta yada a shafinta na Facebook, an bayyana adadin kudade ga kowane bangare.

Nisabin Zakkah, Haddin Sata da Sadaki, da kuma Diyyar rai

A cewar sanarwar, yanzu nisabin Zakkah ya koma N3,918,800, wanda aka kwatanta da darajar farashin kwal a duniya.

A bangaren haddin sata da kuma sadaki na auren mace, dole sai ya kai akalla N48,985 kafin ya cika ka'idar shari'a.

Abin da hakan ke nufi shine, ana yanke hannun barawo ne idan a shari'ance idan ya saci dukiyar da ta kai aalla N48,985.

Yadda batun sadaki yake a shari'ar Muslunci
Hakazalika, a shari'a dole mai neman aure ya ba da sadakin da bai yi kasa da N48,985 ba don cikar ka'idar daurin aure.

A bangaren Diyyar rai, ana daurawa wanda ya yi kisa biyan Diyya ne a kan kudi N195,940,000, duba da darajar kudade da ake dasu a yanzu.

Wadannan na kadan daga cikin hanyoyin da addinin Islama ya tanada don yiwa kowa adalci a fannin gudanar da rayuwar yau da kullum.

Yadda nisabi yake a shekarun baya
A shekarun da suka gabata, majalisar koli ta addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana nisabin karancin sadaki a kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta samu zantawa da Sheikh Khamis Al-Misriy, limamin masallacin Abu Ubaidah Bn Jarrah dake bye-pass jihar Kaduna domin samun karin haske.

Kamar yadda malamin ya sanar, nisabi dai shine wani ma'auni da ake gwadawa domin a gane darajar kudi da inda ya kai. A musulunce kuwa ana kiran shi da kaso daya bisa hudu na dinari daya.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN