Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan gwamnati a yayin bikin Sallah Eid-El-Kabir. Rahotun Jaridar Daily trust.
“Mai martaba yana da mahimmanci majalisar masarautar ta lura cewa mun fara aikin rusau ne domin dawo da kadarorin jama’a da aka mallaka ba bisa ka’ida ba, kuma za mu tabbatar da cewa an dawo da duk irin wadannan kadarorin domin amfanin mutanen Kano nagari.”
"Babu nadama a kan rusa gine-ginen da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta sayar."
Ya kuma yabawa Sarkin da ‘yan majalisar Masarautar bisa wannan ziyara da ta kai irinta ta farko tun bayan hawansa mulki yayin da ya kuma zayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin kwanaki 31 da suka gabata a kan karagar mulki.
Ya bayyana nasarorin da ya samu da suka hada da: biyan kudin NECO ga daliban makarantun sakandare 55,000 da ya kai Naira biliyan 1.5; maido da fitilun tituna; da kuma rage matsalar satar waya a cikin birnin Kano.
Sauran nasarorin, a cewar gwamna Yusuf, sun hada da: sake fara tantancewa don bayar da tallafin karatu na kasashen waje ga ’yan asalin Kano masu digiri na farko; gaggawar biyan albashi da fansho; da kwashe dubban sautunan sharar gida a cikin babban birni.
Gwamnan ya kuma bukaci Uban Masarautar da ya ci gaba da tallafa wa manufofin gwamnatinsa da aka tsara domin kawo ci gaba a jihar da raba ribar dimokuradiyya ga al’ummar jihar.
A nasa bangaren, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce sun kai ziyarar ne domin taya gwamnan murnar bikin Sallah, ya kuma ba da tabbacin a shirye ya ke ya ba da shawarwarin da za su kasance masu muhimmanci da amfani ga ci gaban jihar.
Sarkin ya kuma yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su taimaka wa marasa galihu wajen dakile illolin cire tallafin man fetur.
Published by isyaku.com