Juyin mulkin Nijar bai tabbata ba, dole ne a dawo da shugaban kasa, cewar shugaban Faransa


Faransa ta fada a ranar Juma’a 28 ga watan Yuli cewa kwace iko a Nijar ba ta tabbata ba, kuma har yanzu wadanda ke da hannu a ciki na da lokaci wajen amincewa da bukatun kasashen duniya na a maido da hambararren shugaban kasar.


 Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum na tsare a fadar shugaban kasa kuma har yanzu ba a san ko wanene ke jagorantar kasar ba bayan da sojojin kasar a yammacin Laraba suka shelanta juyin mulkin da ya haifar da tofin Allah tsine. A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban hafsan hafsoshinta, rundunar a ranar Alhamis ta bayyana goyon bayanta ga sojojin da suka tsige shugaba Mohamed Bazoum daga mulki.  Ya ce abin da ya sa a gaba shi ne kaucewa tada zaune tsaye a kasar. Da yake magana da manema labarai a gefen ziyarar da shugaban Faransa Emmanuel Macron zai kai Papua New Guinea, ministan harkokin wajen Faransa.
 Catherine Colonna ya ce akwai yiyuwar kasashen kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka za su gana a ranar Lahadi mai zuwa domin tattaunawa kan kakabawa Nijar takunkumi.


 Faransa ta yi wa Nijar mulkin mallaka har zuwa lokacin da kasar ta samu ‘yancin kai a shekarar 1960. Faransa da Amurka wasu kasashen yammacin duniya ne da ke da dimbin karfin soji da sansanonin soji a Nijar amma akwai rahotannin da ke cewa Rasha na shirin taka kafarta a fagen soja da siyasar kasar. A ranar alhamis, ana iya ganin 'yan kasa suna kona gine-gine na jam'iyya mai mulki tare da wasu mutane dauke da tutocin Rasha da kuma taken goyon bayan Rasha.


 Kafar yada labaran Faransa ta nakalto Colonna na cewa "Idan kun ji na ce yunkurin juyin mulki, saboda ba mu yi la'akari da cewa al'amura sun tabbata ba."


 Colonna ya ce Macron ya yi magana da Bazoum a ranar Juma'a kuma yana cikin koshin lafiya kuma ya kamata a sake shi a matsayin sharadin maido da tsarin mulki.


 "Dole ne a mayar da shugaba Bazoum kan ayyukansa na tsarin mulki," in ji Colonna.


 Wata majiyar diflomasiyyar Faransa ta fada a ranar Alhamis cewa lamarin ya ci gaba da kasancewa cikin rudani

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN